Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaGwamnan Zamfara Dauda Lawal da Minista Bello Matawalle na musayar kalamai kan...

Gwamnan Zamfara Dauda Lawal da Minista Bello Matawalle na musayar kalamai kan matsalar tsaro a jihar

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, da Minista Bello Matawalle, sun yi musayar kalamai kan kalubalen tsaro da sauran matsalolin tattalin arziki da suka addabi jihar.

Rikicin da ya kunno kai tsakanin gwamnan mai ci da wanda ya gada, ya taso ne bayan wata hira da Gwamna Lawal ya tuhumi Matawalle kan yadda ya shugabanci jihar.

Da yake jawabi ga manema labarai a Kaduna, tsohon kwamishinan yada labarai a gwamnatin Matawalle, Ibrahim Dosara, ya zargi Dauda Lawal da zargin cewa shi ne ke da alhakin matsalolin tsaro da tattalin arziki da al’umma ke fuskanta.

Dosara ya ce kamata ya yi a dora wa Dauda alhakin matsalolin tsaro da tattalin arziki da al’ummar Zamfara ke fama da su, inda ya ce Matawalle yana iya kokarinsa don kawo karshen matsalolin tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata