Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnatin jihar Neja ta sa dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a Minna...

Gwamnatin jihar Neja ta sa dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a Minna babban birnin jihar saboda matsalar tsaro

Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya sanya dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a Minna babban birnin jihar, sakamakon yawaitar hare-hare dake ajalin mutane da dama a birnin.

A cewar gwamnan yanzu haka an takaita zirga-zirgar babura da masu tuka keke tsakanin karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe.

Bago ya bayyana hakan ne a yayin wani taro kan tsaro da masu ruwa da tsaki da suka hada da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro wanda ya gudana a gidan gwamnati a Talatar nan.

Sai dai sanarwar ta ce wannan matakin bai shafi fita saboda lalura ta rashin lafiya ba.

Ya bayyana cewa sabon matakin na da nufin dakile matsalolin tsaro da ke kara tabarbarewa a babban birnin jihar.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnati ba za ta zauna a yayin da masu aikata laifuka ke ci gaba da kai hare-hare da ajalin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata