DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za a yi wa matasan NYSC karin kashi 100 na alawus a jihar Zamfara

-

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal na ya ba da umarnin kara yawan alawus-alawus na matasa masu yi wa kasa hidima, NYSC, da za su yi aiki a jihar da kashi 100 cikin 100.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Gusau, yayin da yake bude sansanin masu yi wa kasa hidima Batch ‘A’ na 2025 a jihar.

Google search engine

Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Abubakar Nakwada a wajen taron, ya nanata kudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da jin dadin daukacin mambobin su 550 da aka tura jihar.

A wajen taro ya sanar da cewa an bayar da umarnin a dawo da biyan alawus-alawus tare da karin wani kaso ga duk masu yi wa kasa hidima da ke jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dattawa ta bukaci a dauki matasa aikin tsaro domin magance matsalar tsaro

Majalisar dattawan Nijeriya, ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a ƙasar, tana kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya amince da daukar matasa akalla...

Matukar dimokradiyya ta gaza a Nijeriya sai ya shafi fadin Yammacin Afrika – ECOWAS

Kungiyar tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika, ECOWAS, ta gargadi cewa duk wani rauni da dimokuradiyya ta samu a Nijeriya zai yi sanadin rushewar tsarin a...

Mafi Shahara