DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Farashin shinkafar waje mai nauyin 50KG ya karye a kasuwannin Najeriya

-

Rahoton da kamfanin S&P Global ya fitar ya bayyana cewa farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya sauka zuwa N58,000 a wasu yankunan Najeriya, musamman a kauyuka, sakamakon yawaitar shigo da shinkafa daga Jamhuriyar Benin.

Google search engine

Wannan na zuwa ne bayan kasar India ta cire harajin fitar da shinkafa irinta parboiled, wanda ya sa kasuwar shinkafa ta Yammacin Afirka ta fuskanci koma baya.

A cikin shekarar 2024 gaba daya, India ta fitar da tan miliyan 5.35, idan aka kwatanta da tan miliyan 3.9 na 2023. Inda rahoton yace har yanzu Najeriya na ci gaba da shigo da shinkafa ta Jamhuriyar Benin ta barauniyar hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babban hafsan sojin kasa ya umurci sojoji da su tsaurara wajen ganin sun ceto dalibai mata da aka sace a jihar Kebbi

Babban hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya umarci dakarun Operation Fansan Yamma da su matsa kaimi wajen ceto daliban GGCSS Maga da...

’Yan bindiga sun sace fasinjoji shida a hanyar Ogobia–Adoka a Benue

’Yan bindiga sun tare wata motar haya suka tafi da fasinjoji shida sannan suka kashe direba a hanyar Ogobia–Adoka da ke ƙaramar hukumar Otukpo a...

Mafi Shahara