Thursday, April 9, 2026
HomeLabaraiMajalisun tarayyar Nijeriya sun dage tattaunawa kan bukatar Shugaba Tinubu kan jihar...

Majalisun tarayyar Nijeriya sun dage tattaunawa kan bukatar Shugaba Tinubu kan jihar Rivers

Majalisar dattawa ta dage yin muhawara kan dokar ta-baci da shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa a jihar Rivers zuwa ranar Alhamis, hakama a majalisar wakilai ba a yi muhawara ba kan batun, duk da tabbacin da majalisar ta bayar da farko.

Binciken jaridar Punch ya gano cewa an dage zaman ne saboda rashin halartar da yawa daga cikin ‘yan majalisar ba, lamarin da ya sa aka kasa samun yawan ‘yan majalisar da ake bukata.

A daren jiya Talata ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas, inda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata