Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da dokar haraji da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar wa majalisar a watan Oktoban 2024, domin yi mata garambawul.
A ranar Alhamis din makon jiya ne majalisar ta yi nazari tare da amincewa da shawarwarin rahoton kwamitin kudi na majalisar, musamman a wuraren da ake ta cece-kuce da su kamar harajin VAT da kuma harajin gado
Yanzu dai majalisar dattawa ake jita ta amince da kudirin kafin a mika shi ga ga shugaban kasa domin sanya hannu ga sabbin dokokin na haraji.




