Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiHukumar EFCC ta kama wani dan TikTok kan zargin wulakanta takardun Naira...

Hukumar EFCC ta kama wani dan TikTok kan zargin wulakanta takardun Naira a cikin bidiyonsa

Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC shiyyar Kaduna, sun damke wani matashi Muhammed Kabir Sa’ad bisa zarginsa da wulakanta takardun Naira.

Sa’ad ya wallafa bidiyonsa a shafinsa na TikTok da Instagram inda aka gan shi yana watsi da takardar Naira a kasa tare da tattaka, inda kuma ya kalubalanci jami’an EFCC su kama shi idan za su iya.

A wata sanarwar da ta wallafa a Facebook, hukumar EFCC ta ce an kamo matashin a unguwar Tudun Wada da ke Jihar Kaduna, kuma an kai shi hedkwatar hukumar ta Kaduna domin yi masa tambayoyi.

Hukumar ta ce za a gurfanar da shi gaban kotu idan aka kammala bincike.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata