![]() |
Sule Lamido |
Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, yayi watsi da kiran da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi na neman shugabannin jam’iyyar adawa su koma jam’iyyar SDP.
El-Rufai, wanda a kwanakin baya ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa SDP, ya yi wannan kiran ne a wata hira da BBC Hausa.
Wanda a yayin hirar bai ambaci sunan Sule Lamido ba, ya gayyaci manyan ‘yan adawa da suka hada da Atiku Abubakar, da Peter Obi, da Rotimi Amaechi, da Rauf Aregbesola, domin su dawo jam’iyyar SDP.
Da yake mayar da martani a wata hira ta da BBC Hausa ta yi a ranar Lahadi, Lamido ya yi watsi da gayyatar da aka yi masa a matsayin cin fuska, inda ya ce jam’iyyar PDP ce ta taimaka wajen kafa harsashin siyasar El-Rufai.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP ita ce ta haifi tsohon gwamnan Kaduna El-Rufai,kuma ba za su bar PDP ba.