Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaMajalisar tarayya na shirin kafa wani kwamitin sulhu mai ƙarfi da zai...

Majalisar tarayya na shirin kafa wani kwamitin sulhu mai ƙarfi da zai shiga tsakani don warware rikicin siyasa a Jihar Rivers.

Shugaban majalisar wakilai, honarabul Abbas Tajudeen, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da majalisar ta koma bakin aiki, bayan hutun bukukuwan Easter da Sallah.

Rikicin ya samo asali ne tsakanin Gwamnan Jihar Rivers da aka dakatar, Siminalayi Fubara, da tsohon ubangidansa a siyasa, kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

Abbas ya ce kwamitin da za a kafa tare da hadin gwiwar Majalisar Dattawa zai kunshi manyan ‘yan kasa masu kima da mutunci, wadanda za su jagoranci tattaunawa, su samar da zaman lafiya tare da dawo da tsarin dimokiradiyya a Jihar Rivers da sauran jihohin da ke fuskantar rikice-rikice irin wannan.

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, shi ne zai shugabanci kwamitin sulhun. Daga cikin mambobin kwamitin akwai Sanata Adamu Aliero daga Jihar Kebbi, Sanata Osita Izunaso daga Imo, Sanata Osita Ngwu daga Enugu, Sanata Kaka Shehu daga Borno, Sanata Aminu Abass daga Adamawa, Sanata Tokunbo Abiru daga Legas, da Sanata Adeniyi Adegbonmire daga Jihar Ondo.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata