Sunday, April 5, 2026
HomeKetareDan Amurka na farko a tarihi Robert F. Prevost ya zama sabon...

Dan Amurka na farko a tarihi Robert F. Prevost ya zama sabon Fafaroma

Robert Francis Prevost, dan asalin birnin Chicago a Amurka, an haife shi a ranar 14 ga Satumba, 1955, yana da shekaru 69 a yanzu.

An nada shi a matsayin sabon shugaban Ma’aikatar Bishop-Bishop da kuma Shugaban Hukumar Paparoma kan Latin America a cocin Katolika.

Prevost, wanda memba ne na Darikar Saint Augustine, ya shafe shekaru da dama yana aikin mishan a Peru, inda ya rike mukamai daban-daban kafin daga bisani ya zama bishop na Chiclayo.

A shekarar 2023, Paparoma Francis ya nada shi Kardinal, sannan daga baya ya dora masa nauyin jagorantar daya daga cikin manyan ma’aikatun cocin Katolika a Vatican, yanzu kuma ya zama sabon Fafaroma bayan rasuwar Fafaroma Francis wanda za’a rinka kiransa Fafaroma Leo na 14.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata