Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiBa gasa muke yi da kamfanin NNPCL ba - Dangote

Ba gasa muke yi da kamfanin NNPCL ba – Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa matatar man fetur dinsa ba ta yin gasa da Kamfanin man Fetur na Nijeriya, wato NNPC.

Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa sabon shugaban rukunin NNPC, Injiniya Bayo Ojulari, a hedkwatar kamfanin da ke Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun NNPC, Olufemi Soneye, ya fitar a yau Jumma’a, Dangote ya ce akwai bukatar haɗin gwiwa domin tabbatar da samar da makamashi mai ɗorewa a ƙasar nan.

Ziyarar, a cewar Soneye, na cikin matakan da ake ɗauka domin ƙarfafa dangantaka da fahimtar juna tsakanin manyan kamfanonin mai biyu—na gwamnati da na masu zaman kansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata