Ministan babban birnin Nijeriya Nyesom Wike, ya bayyana cewa jam’iyyarsa, wato PDP, ba za ta iya samun nasarar lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2027 ba idan har ba ta sauya tsarin rabon mukamai ‘zoning’ nata ba.
Ministan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai, inda ya nuna rashin bin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar dangane da tsarin rabon shugabancin jam’iyya da kuma takarar shugaban kasa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na jam’iyyar PDP, Adolphus Wabara, ya karbi tsoffin gwamnoni Samuel Ortom na Jihar Benue, Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu da wasu mutum 38 cikin Kwamitin Amintattu na jam’iyyar.
