DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Da kamar wuya PDP ta rayu har 2027 – Tsohon Gwamnan Benue Gabriel Suswan

-

Tsohon Gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam, ya yi gargadin cewa jam’iyyar PDP na iya rushewa kafin zaben 2027 idan shugabanninta ba su dauki matakan gyara matsalolinta ba cikin gaggawa.

Jam’iyyar PDP na cikin rikici kan wanda ya kamata ya rike mukamin sakataren jam’iyya na kasa.

Haka kuma, jam’iyyar ta fuskanci sauyin salo a ‘yan kwanakin nan, bayan da Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da wanda ya gada, Sanata Ifeanyi Okowa, tare da wasu tsofaffin shugabanni da mambobin jam’iyyar PDP suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Da yake magana a shirin The Morning Show na Arise TV, Suswam ya ce jam’iyyar PDP na cikin mawuyacin hali.

Ya bayyana cewa, da dama daga cikin mambobin jam’iyyar sun rasa kwarin gwiwa kuma suna jin ba za ta iya kai labari ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Barayin daji sun saci wani shugaban jam’iyyar APC, sun nemi a ba su kudin fansa Naira milyan 100

Wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace wani shugaban jam’iyyar APC na gundumar Ward 5 da ke Ifon, a karamar hukumar Ose...

Kotu a Kano ta ki karbar bukatar Ganduje ta dakatar da shari’ar zargin cin hanci

Wata babbar kotu a jihar Kano ta yi watsi da wata bukata da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje, ya shigar domin kalubalantar...

Mafi Shahara