Jiga-jigan jam’iyyar APC a Arewa maso Yammacin Nijeriya sun sanar da matsayarsu da ke cewa suna goyon bayan Shugaba Tinubu ya yi tazarce a babban zaben shekarar 2027 da ke tafe.
A taron masu ruwa da tsaki da suka gudanar a Kaduna, jiga-jigan da suka hada da gwamnoni, Sanatoci, masu rike da mukamai a fadar shugaban kasa, sun ce sun gamsu da salon mulkin Shugaba Tinubu, shi ya sa suka amince da ya yi tazarce a zabe mai zuwa.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai gwamnonin jihohin Kebbi, Kaduna da Jigawa. Kazalika akwai kuma Sanata Atiku Bagudu, Badaru Abubakar, Sanata Barau Jibrin da Tajuddeen Abbas.
