Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaWike ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu a zaben 2027

Wike ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu a zaben 2027

Ministan Abuja Nyesom Wike, ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa yana iya kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 idan jam’iyyar PDP ta ware tikitin shugaban kasa zuwa Kudu.

Ya tabbatar da biyayyarsa ga gwamnatin Tinubu, yana mai cewa bai da niyyar tsayawa takara da mutumin da yake yi wa aiki.

A wata hira da ya yi da BBC News sashen Pidgin, Wike ya ce, ba zai tsaya takara ba. Ya diga alamar tambayar cewa me zai sa ya tsaya takara da wanda yake yi wa aiki?.

Yayin da yake jaddada goyon bayansa ga Tinubu, Wike ya ce a halin yanzu babu wani dan adawa mai karfi da zai iya kawar da shugaban kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata