Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa ido da ido ya bukaci Janar Ibrahim Babangida da ya sauka daga mulki bayan soke zaben shugaban kasa na 1993 da MKO Abiola ya lashe.
A cikin littafinsa Being True to Myself da aka kaddamar a 13 ga Mayu, Lamido ya wallafa cewa Babangida ya ce babu wanda zai iya fada masa haka a fuskarsa.
A babi na 7 na littafin, Lamido ya tuna yadda aka kira shi zuwa fadar shugaban kasa, inda ya bayyana rashin gamsuwarsa da dalilan da Babangida ya bayar kan soke zaben.
