Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaShugabannin Kudu maso Gabas na shirin taron marawa Tinubu bayan tazarce a...

Shugabannin Kudu maso Gabas na shirin taron marawa Tinubu bayan tazarce a takarar 2027 — Umahi

Ministan Ayyuka kuma tsohon Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana cewa shugabannin yankin Kudu maso Gabas, ciki har da gwamnonin jihohi biyar na yankin, na shirin gudanar da babban taro domin bayyana goyon bayansu ga shugaba Bola Tinubu domin tazarce a zaben 2027.

Umahi ya bayyana hakan ne a cikin wani shiri na musamman da za a gabatar a fadar shugaban kasa domin bikin cika shekara biyu da mulkin Tinubu, kamar yadda mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana.

A zaben 2023, Tinubu ya sha kaye a dukkan jihohin Kudu maso Gabas da suka hada da: Anambra, Ebonyi, Enugu, Imo da Abia, inda ya samu ƙasa da kashi 10 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata