Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiShugaba Tinubu ya aika kudurin kasafin kudin jihar Rivers da ya kai...

Shugaba Tinubu ya aika kudurin kasafin kudin jihar Rivers da ya kai Tiriliyan 1.48 ga majalisar tarayya

Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika kudirin kasafin kudin jihar Ribas na Naira tiriliyan 1.48 ga majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi a wannan Alhamis.

Shugaban ya ce an yi kudirin kasafin saboda soke kasafin kudin jihar na 2025 da kotun koli ta yi da kuma ayyana dokar ta-baci a jihar.

Shugaban ya ce za a kashe bilyan 324 daga cikin kudin wajen samar da ababen more rayuwa, inda aka ware Naira biliyan 166 ga fannin kiwon lafiya, yayin da za a kashe biliyan 75.6 kan harkar ilimi da kuma biliyan 31.4bn bangaren noma.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata