Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya bukaci kwamishinoni da masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa da su bi sahunsa su koma jam’iyyar APC, ko su yi murabus.
A cikin wani taron majalisar zartarwa, Eno ya tabbatar da shirin sauya shekar sa, yana mai cewa duk wanda bai shirya bin sa ba, ya tanadi barin mukaminsa ranar da ya sanar da sauya shekarsa.
Ya ce ba sabon labari bane cewar zan sauya sheka daga PDP zuwa APC, ko da yak eina martaba PDP a matsayinta na dandamalin da ya daga daraja ta zuwa matsayin da nake kai yanzu.
