Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya ce gwamnoni ba za su goyi bayan soke Hukomomin Zabe na Jihohi (SIECs) ba, yana mai cewa kamata yayi a gyara su maimakon a rushe su.
Daily Trust ta ruwaito gwamna Sule na cewa matsalolin SIECs sun hada da tsoma baki a siyasa, karancin kudi da rashin amincewar jama’a, kalubalen da yace hatta hukumar INEC na fama da su.
Inda ya kara da cewa akwai bukatar rinjayar da siyasa da ke haddasa kiran a soke SIECs, yana mai fatan taron zai samar da mafita kuma gwamnoni za su goyi bayan shawarwari masu amfani.
