Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiAna ci gaba da dora ayar tambaya kan rufe matatar Fatakwal da...

Ana ci gaba da dora ayar tambaya kan rufe matatar Fatakwal da ta lakume sama da Naira Tiriliyan daya 1.5

Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya sanar da rufe matatar mai ta Fatakwal (PHRC) daga ranar Asabar domin gudanar da gyare-gyare da duba lafiyar aikin injina a matatar.

Wannan na zuwa watanni shida bayan fara aikin dakon mai daga matatar bayan kashe dala biliyan 1.5 wajen gyaranta.

Jami’in hulɗa da jama’a na NNPCL, Femi Soneye, ya ce rufewar na cikin tsare-tsaren kiyayewa da tabbatar da ingancin aiki a matatar.

Masana masana’antu da wasu masu ruwa da tsaki sun nuna damuwa, suna kuma kira da a sayar da matatun gwamnati gaba ɗaya don samun inganci da cikakken amfanin su ga Nijeriya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata