A ranar Litinin ne wasu matasa suka kona wani bangare na ofishin ‘Yansandan da ke Rano a jihar Kano bayan mutuwar wani Abdullahi Musa da ake zargi a caji ofis.
An kama Abdullahi Musa ne a ranar Lahadi bisa zargin aikata laifin karya dokar amfani da hanya.
Dalilin haka ne wasu fusatattun matasa suka fito zanga-zangar lumana inda daga bisani abin ya canza salo sakamakon halbi da ‘yansandan suka yi cikin masu zanga-zangar, lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutane 2, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘Yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wani bangare na ofishin ‘Yansandan ne masu zanga-zangar suka lahanta.
