Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen cewa za a tafka ruwan sama da tsawa a wasu sassan kasar daga ranar Litinin zuwa Laraba.
Wani bayani da NiMet ta fitar ranar Lahadi a Abuja ta yi hasashen za a yi ruwan sama a wasu sassan jihohin Taraba, Kaduna, Gombe, Bauchi, Kebbi, Sokoto, Katsina, Jigawa da Kano a yankin arewa.
A cewar hukumar, za a iya samun tsawa da ruwan sama a wasu sassan jihohin Plateau, Babban Birnin Tarayya, Nasarawa, Kwara, Neja, Kogi, da Jihohin Benue.
