Wata kotun majistare da ke Osogbo a jihar Osun, ta tasa keyar wani matashi mai suna Taofeek Jimoh a gidan yari na Ilesa bisa zargin hallaka mahaifiyarsa.
Jimoh, wanda ba a ka gurfanar ba tare da lauya mai kare ba, ana tuhumarsa da laifin kisan kai.
Mai gabatar da kara, ASP Fatoba Temitope, ta shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne da misalin karfe 8 na daren ranar 19 ga watan Fabrairu a Oke-Ola, Osogbo.
Temitope ya ce wanda ake tuhumar ya doki mahaifiyarsa, Taibat Jimoh rauni, bayan wata jayayya da suka yi, kuma hakan ya yi sanadin mutuwarta.
Alkalin kotun, Mista O. Olatunji, ya ce za a ci gaba da tsare Jimoh har zuwa ranar 17 ga watan Yuni, inda za a ci gaba da sauraren karar.
