Wasu mutane da ake zargin masu jari bola ne sun caka wa wani mutum mai suna Nwangwu Onyebuchi Clement wuka har lahira a yankin Kutunku da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja.
Wani mazaunin yankin mai suna Francis Nnamdi ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:26 na safe lokacin da masu jari bola su uku suka shiga gidan marigayin, tare da kokarin cire tagogin gidansa.
Ya ce mai gidan da ya gansu sai ya tambaye su dalilin da ya sa suke kokarin cire masa tagogi, daga nan ne daya daga cikin ‘yan masu satar ya zaro wuka ya caka masa.
Ya kara da cewa shima mutumin wanda ke rike da adda, ya daba wa daya daga cikinsu sara a bayansa.
Da jaridar Daily Trust tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, a wani sako da ta aike mata ta ce ba ta da labarin faruwar lamarin amma za ta bincika.
