Monday, April 6, 2026
HomeKetareFursunoni 200 sun arce daga gidan yarin kasar Pakistan

Fursunoni 200 sun arce daga gidan yarin kasar Pakistan

Jami’ai a kasar Pakistan sun bayar da rahoton cewa fiye da fursunoni 200 sun tsere daga gidan yari a birnin Karachi bayan da aka bar su su fita daga dakunansu sakamakon girgizar kasa da aka ji sau da dama a yankin.

Zia-ul-Hasan Lanjar, kwamishinan shari’a na jihar, ya shaida wa ’yan jarida a wurin cewa an bai wa daruruwan fursunoni damar fita zuwa harabar gidan yari saboda girgizar kasar.

Farkon tserewar fursunonin ya faru ne da daren Litinin kafin karfe 12 na dare, kuma ya ci gaba har zuwa wayewar garin Talata, in ji kwamishinan.

’Yan sanda sun ce fursunonin sun kwace bindigu daga hannun ma’aikatan gidan yari, abin da ya janyo musayar wuta, kafin daga bisani su tilasta a bude kofar shiga ta gaba.

A ranar Talata, wani wakilin kamfanin Reuters da ke wurin ya ga tagogi fasassu da kuma na’urorin lantarki da suka lalace a cikin gidan yari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata