Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAna kiyasin kashe Naira bilyan 880 don gyaran hanyoyi a Nijeriya duk shekara

Ana kiyasin kashe Naira bilyan 880 don gyaran hanyoyi a Nijeriya duk shekara

Ministan kasa a ma’aikatar ayyuka Mohammed Goroyo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na bukatar kashe kimanin naira biliyan 880 a duk shekara domin gyaran titunan kasar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da manajan darakta na hukumar kula da titunan ta tarayya, Chukwuemeka Abbasi ya bayyana cewa, har yanzu hukumar kula da hako danyen mai da sayar da mai ta Nijeriya ba ta fara aiwatar da tsarin cire harajin hanyoyi a kudin man fetur da dizal ba.

Jami’an gwamnatin biyu sun yi wadannan kalaman ne a Abuja, yayin wani zaman bincike da kwamitin majalisar wakilai na wucin gadi ya yi.

Kwamitin na binciken kan yadda ake aiwatar da tsarin biyan kashi biyar bisa dari na masu amfani da hanyoyin mota a karkashin hukumar kula da tituna ta tarayya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata