Gwamnan jihar Neja Umar Bago ya dakatar da duk wasu tarukan Sallah da suka hada da Hawan Bariki, da sauran tarukan jama’a da ake yi a yayin bikin sallah.
A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Usman ya fitar a ranar Laraba, ya ce wannan umarni na zuwa ne biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a Mokwa, inda iyalai da dama suka rasa matsugunansu tare da rasa rayukansu.
Sanarwar ta ce an dauki wannan matakin ne a matsayin taya jimami ga wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafa a Mokwa.
