Monday, April 6, 2026
HomeKetareShugaba Trump na Amurka ya haramta wa 'yan kasashe 12 shiga kasar

Shugaba Trump na Amurka ya haramta wa ‘yan kasashe 12 shiga kasar

Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka ta haramta wa ‘yan kasashe 12 shiga Amurka.

Kasashen da abin ya shafa sun hada da Afghanistan, Myanmar, Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan da Yemen.

Duk wani dan ƙasa daga waɗannan ƙasashe za a hana su cikakkun takardun shiga Amurka, kamar yadda sanarwar ta ce.

Kazalika, za a takaita shigar ‘yan kasashen Burundi, Cuba, Laos, Saliyo, Togo, Turkmenistan da Venezuela.

Trump ya ce ana bukatar daukar matakin ne domin kare Amurka daga ‘yan ta’adda na kasashen waje da sauran barazanar tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata