Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaPDP ce har yanzu jam'iyyar adawa mafi tasiri a Nijeriya - Bukola...

PDP ce har yanzu jam’iyyar adawa mafi tasiri a Nijeriya – Bukola Saraki

Tsohon Shugaban Majalisar dattawan Nijeriya, Bukola Saraki, ya ce jam’iyyar PDP ce har yanzu jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a Nijeriya.

Ya ce PDP tana da ƙarfi kuma za ta iya ƙalubalantar jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027 da ke tafe saboda orin tasirin da take da shi.

Saraki, wanda ke jagorantar Kwamitin Sulhu na jam’iyyar PDP, ya faɗi haka ne a wani taro da ya yi da shugabannin jam’iyyar a Ilorin babban birnin jihar Kwara.

Sai dai a jawabinsa ya amince cewa wasu sun bar jam’iyyar, amma mutane da dama suna ci gaba da shigowa jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata