DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Karamin Minstan gidaje da raya birane ya yi barzanar ficewa daga APC

-

Yusuf Abdullahi Ata

Karamin Ministan gidaje da raya birane Yusuf Abdullahi Ata, ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC idan har jam’iyyar ta ci gaba da barin Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar reshen jihar Kano.
Yusuf  Abdullahi Ata ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron jiga- jigan jam’iyyar APC na karamar hukumar Fagge a Kano ranar Asabar, gabanin taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar  a Abuja wanda za a yi mako mai zuwa.
Ata ya ce jam’iyyar ta fadi zabe a 2023 ne saboda irin  kalaman shugaban jam’iyyar da ke wasu maganganu marasa dadi.Ata, wanda tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano ne, ya ce APC za ta ci zabe idan shugabancinta ya kasance mai gaskiya da kuma amana da yarda da Allah ne kadai ke ba da mulki ga wanda ya so.
Ministan ya ce  idan aka ci gaba da rike shugabannin jam’iyyar da ake dasu yanzu,  tabbas za su fice daga jam’iyyar kuma jam’iyyar za ta sake yin rashin nasara.Ind ya ce ba sa tare da irin wadannan mutane, kuma ko me ya faru, ba za su daidaita da su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Atiku Abubakar ya caccaki hukumar EFCC kan tsare tsohon dan majalisa Gudaji Kazaure

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, kan tsare tsohon dan...

Gwamnatocin Pakistan da Indiya sun amince da tsagaita wuta a Asabar dinnan

Ministan harkokin wajen Pakistan Ishaq Dar ya sanar a shafinsa na X cewa, kasashen sun amince da Shirin tsagaita wuta cikin gaggawa. Shugaba Trump ya sanar...

Mafi Shahara