Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Borno ta bayar da tallafin Naira miliyan 300 ga mutanen da...

Gwamnatin Borno ta bayar da tallafin Naira miliyan 300 ga mutanen da ambaliyar Mokwa ta shafa a jihar Neja

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya sanar da bayar da tallafin a lokacin da ya jagoranci tawagar jihar a ziyarar jaje a gidan gwamnati dake Minna.

Ya ce an bayar da tallafin ne domin kara wa kokarin gwamnatin jihar Neja wajen magance kalubalen da aka fuskanta.

Da yake jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Neja, Farfesa Zulum ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata gwamnatocin kasashen duniya su hada karfi da karfe domin dakile illolin sauyin yanayi a cikin al’umma.

Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da ingantaccen tsari wanda zai duba tare da magance matsalar sauyin yanayi a fadin kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata