DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Akwai bukatar hukumar NAHCON ta mayar wa maniyyatan hajjin bana naira 400,000 – Kungiyar IHR

-

Kungiyar “Independent Hajj Reporters” mai sanya ido kan harkokin aikin hajji ta yi kira ga hukumar alhazzan Nijeriya da ta mayar wa maniyyata aikin hajjin bana naira N437,000 kowannensu, bayan da aka samu saukar farashin dala a kasuwar canji.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce binciken da ta yi akan bayanan kudin aikin hajjin 2025 da hukumar NAHCON ta fita, ta gano cewa ya kamata kowane maniyyaci a mayar masa da rarar kudin da ya biya.
Sai dai a martanin da suka mayar, bangaren yada labarai na hukumar NAHCON sun bayyana cewa, sabanin fahimtar kungiyar IHP duk wani sauyi da aka samu a canjin kudi bayan an kayyade kudin aikin hajji, kai tsaye ba ya nufin za a mayar wa mahajjata kudin.
Bangaren yada labaran sun kara da cewa hukumar NAHCON ta yi alkawalin bin ka’ida wajen mayar wa mahajjata kudin su idan aka samu wani ragi.

 

Google search engine

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ramaphosa ya yi Allah-wadai da kama Maduro da Amurka ta yi

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta ɗauka na kama Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro. Ramaphosa ya...

Sojoji sun ceto mutane shida da aka sace a Kaduna

Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun samu nasarar ceto mutane shida da aka sace a wani sumame da suka gudanar a yankunan Kajuru da Kujama...

Mafi Shahara