Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaGwamnatin shugaba Tinubu ta gaza - Baba-Ahmed

Gwamnatin shugaba Tinubu ta gaza – Baba-Ahmed

Tsohon mai bai wa shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa Hakeem Baba-Ahmed, ya ce gwamnati mai ci ta kasa inganta rayuwar talakawan Nijeriya da kuma yadda ake gudanar da mulki.

Baba-Ahmed ya ce gwamnatin Tinubu ta saba alkawarin inganta rayuwar talakawan Nijeriya.

Tsohon kakakin kungiyar dattawan Arewa ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata, inda ya ce a bayyane yake, gwamnatin Tinubu ta gaza kamar yadda aka yi tsammanin cewa za samar da ingantaccen shugabanci.

A cewarsa, cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi ya yi tasiri sosai ga canza rayuwar talakawan Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata