Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKotun daukaka kara ta dakatar da shari'ar da Natasha ta shigar inda...

Kotun daukaka kara ta dakatar da shari’ar da Natasha ta shigar inda take kalubalantar dakatarwar da majalisar dattawa ta yi mata

Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, ta bayar da umarnin dakatar da ci gaba da shari’ar da ake yi a babbar kotun tarayya, wadda Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar, tana kalubalantar dakatar da ita daga majalisar dattawa.

Kotun daukaka kara ta yanke hukuncin ne ya biyo bayan bukatar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya gabatar, na neman a kara masa wa’adin daukaka kara, kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke, a cewar jaridar Premium Times.

A hukuncin da ya yanke a ranar 10 ga Maris, Alkali Obiora Egwuatu, ya umurci shugaban majalisar dattawa da sauran mutane uku da Natasha ke kara, cikin sa’o’i 72 su bayyana dalilin da zai hana kotun dakatar da duk wani bincike da ake yi wa Natasha a wancan lokacin.

Sai dai Akpabio ya daukaka kara ta hannun lauyansa, inda yanzu kotun daukaka kara ta dakatar da umurnin na farko.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata