Tsohon ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya soki gwamnatin Tinubu da cewa ta fi mayar da hankali kan siyasa fiye da yin aikin da zai amfani jama’a.
A jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya a Abuja, Obi ya ce Najeriya ba ta cikin sahihiyar dimokuraɗiyya saboda talauci ya ƙaru daga 38.9 zuwa 54, kuma yawancin asibitocin ƙananan lafiya ba sa aiki.
Obi ya bayyana cewa yadda yunwa da matsalolin tattalin arziki ke yawaita, yayin da gwamnati ta ci bashin da ya kai har Naira tiriliyan 188.
