Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiNi ne na lashe zaben shugaban Nijeriya a 1999, ba Obasanjo ba...

Ni ne na lashe zaben shugaban Nijeriya a 1999, ba Obasanjo ba – Olu Falae

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a 1999, Chief Olu Falae, ya bayyana cewa shi ne ya lashe zaɓen, ba Olusegun Obasanjo ba, yana mai cewa an murɗe masa sakamako.

A wata hira da aka yi da shi a Arise TV yayin ranar Dimokradiyya, Falae ya ce lauyansa marigayi Chief J.O.K. Ajayi ya tabbatar masa da cewa ya doke Obasanjo da ƙuri’u fiye da miliyan ɗaya.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar, wanda ya tsaya takara karkashin haɗin gwiwar AD da APP, ya ce sun yarda da sakamakon ne domin hana ƙasar komawa rikici, amma yanzu lokaci ya yi da gaskiya za ta bayyana.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda babu sahihin zaɓe a Najeriya tun bayan na 1993.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata