Shahararren ɗan barkwanci, Ali Baba, ya ce tsadar takarar siyasa a Najeriya na janyo cin hanci da rashin gaskiya, inda siyasa ta koma wata hanyar zuba jari maimakon hidima ga jama’a.
A wata hira da aka wallafa a Instagram, ya bayyana cewa takarar Sanata yanzu na bukatar tsakanin Naira biliyan 1.2 zuwa 2, Majalisar Wakilai biliyan 1, da miliyan 500 don Majalisar Jiha.
Haka zalika, ya ce takarar Gwamna a jihohin kamar Delta da Rivers na bukatar biliyan 20 zuwa 25, yayin da a Arewa ke bukatar biliyan 4 zuwa 6.
Jaridar Punch ta ruwaito shi yana cewa wannan yanayi ne ke tilastawa gwamnati rashin mai da hankali kan inganta muhimman sassa kamar ilimi da lafiya.
