Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiFadar shugaban Nijeriya ta musanta bai wa Aisha Yesufu lambar karramawa

Fadar shugaban Nijeriya ta musanta bai wa Aisha Yesufu lambar karramawa

Fadar Shugaban Ƙasa ta karyata wani jerin sunaye da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa an bai wa Aisha Yesufu da wasu mutum 35 lambar karramawa daga hannun Shugaba Bola Tinubu.

Sunayen da suka fara yawo tun ranar Juma’a sun jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman magoya bayan gwamnatin Tinubu, sakamakon saka sunan Aisha Yesufu, fitacciyar ‘yar fafutukar kare haƙƙin ɗan adam da ke sukar gwamnati akai-akai.

A ranar Alhamis, 13 ga Yuni, Shugaba Tinubu ya bayyana sunayen mutane 66 da aka karrama a jawabinsa na Ranar Dimokuraɗiyya da ya gabatar a gaban zaman hadin gwiwar Majalisar Tarayya da ke Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Mai taimaka wa Shugaban Tinubu kan harkokin yada labarai, Temitope Ajayi, ta ce sunayen da ke yawo ba na gaske ne ba kuma ba su da alaƙa da fadar Shugaban Ƙasa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata