DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Dan marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu

-

Abdulmannan Abubakar Giro Argungu ya rasu a wannan Asabar, kusan shekaru biyu bayan rasuwar mahaifinsa.

Matashin shi ne da na tara cikin‚ ‘ya’yan babban malamin addinin Musulunci, Marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu.

Google search engine

A wata hira da DCL Hausa ta yi da shi a 2024, matashin, ya ce ya koyi gudun duniya da riko da addini daga mahaifinsa wanda ya rasu a watan Satumba na 2023

Abdulmannan ne dai ke jagoran masu kula da shafin sada zumunta na marigayi Sheikh Abubakar Giro.

Matashin da ya kammala karatun digirinsa jami’ar Maryam Abacha ya rasu ne bayan fama da gajeruwar jinya. An jima da karfe 2:30pm ake sa ran yi masa jana‘iza a garin Argungu, jihar Kebbi.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu is a highly skilled and experienced broadcast journalist and fact-checker. Ukashatu has over five years of experience in writing, editing, and presenting news and program content for radio and television. As a dedicated and hardworking professional, He is committed to upholding the values of accuracy, fairness, balance, independence, and accountability in her reporting and programs.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An shiga wata na biyu a gyaran matatar mai ta Fatakwal

Matatar mai ta Port Harcourt da ke karkashin kamfanin man Nijeriya NNPCL ta kwashe fiye da wata guda a rufe saboda gyara, ba ta dawo...

Ba mu tsawaita wa’adin hidimta wa kasar matashiyar da ta caccaki Shugaba Tinubu ba – NYSC

Hukumar NYSC ta karyata zargin tsawaita wa wata ‘yar bautar ƙasa daga Legas, Rita Uguamaye (Raye), aikin watanni biyu saboda sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Raye...

Mafi Shahara