Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMajalisar dattawa na shirin ƙara yawan alkalai a kotun kolin Nijeriya zuwa 30

Majalisar dattawa na shirin ƙara yawan alkalai a kotun kolin Nijeriya zuwa 30

By Salim Muhammad Gali

Majalisar dattawa ta Nijeriya na duba yiwuwar ƙara yawan alkalai a kotun kolin kasar daga 21 zuwa 30, domin rage yawan shari’u da ke taruwa a gaban kotun da kuma saurin yanke hukunci.

Wannan na zuwa ne bayan wani kudiri da Sanata Osita Izunaso daga Imo ta Yamma ya gabatar, yana mai bayyana cewa alkalai 21 ba su wadatar ba, duk da an nada su tun 2023.

Sanata Izunaso ya ce adadin alkalai 30 zai ba da damar kafa kwamitoci fiye da hudu a lokaci guda, wanda hakan zai taimaka wajen gudanar da shari’u cikin gaggawa.

Ya kuma yi kira da a dakatar da karɓar ƙananan shari’u a kotun koli, kamar rikicin fili, da saki, yana mai cewa irin waɗannan su rika tsayawa a kananan kotunan.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata