Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiRundunar 'yan sanda ta tsawaita wa’adin lasisin gilashin mota mai duhu zuwa...

Rundunar ‘yan sanda ta tsawaita wa’adin lasisin gilashin mota mai duhu zuwa 12 ga Agusta

By Salim Muhammad Gali

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta tsawaita wa’adin fara tilasta yin lasisin gilashin mota mai duhu wato tinted glass permit zuwa 12 ga Agusta, 2025.

Babban Sufeto Janar, Kayode Egbetokun, ya bayyana haka a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar.

A cewarsa, an ɗauki wannan matakin ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a dake neman sauƙaƙa tsarin neman lasisin.

Rundunar ta ce za a inganta tsarin ta hanyar neman lasisin ta intanet domin rage tsaikon da ake samu.

Haka kuma, an bukaci ’yan Najeriya da su yi amfani da shafin wajen nema ko sabunta lasisin tare da kai rahoton duk wata matsala da suka fuskanta.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata