Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKu shirya don tunkarar 'yan ta'adda da masu tada kayar baya -...

Ku shirya don tunkarar ‘yan ta’adda da masu tada kayar baya – Sakon shugaban sojan Nijeriya ga sabbin sojoji

Shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bukaci sabbin sojoji da suka kammala karbar horo a makarantar horon aikin soja “Depot Nigerian Army” da ke Zariya, Jihar Kaduna, da su kimtsa domin yakar ta’addanci da ’yan tawayen da ke addabar ƙasar.

A jawabinsa ga sabbin sojoji 6,195, Oluyede ya ja hankalinsu da su kasance jarumai, masu aiki da kwarewa kuma masu juriya a fagen daga.

Ya tunatar da su cewa rayuwar soja tana buƙatar sadaukarwa da kishin ƙasa, yana mai nanata cewa aikinsu ne kare martabar Nijeriya.

Oluyede, ya kuma jaddada muhimmancin kiyaye dabi’un rundunar soji irin su ladabi, biyayya, gaskiya, sadaukarwa, jaruntaka da mutunta jama’a.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata