Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da wasu fitattun ’yan jam’iyyar adawa ta PDP a fadarsa da ke Aso Rock a daren Asabar.
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ne ya jagoranci abokan siyasarsa da suka haɗa da tsoffin gwamnonin G5, waɗanda suka ƙi juyawa PDP baya a zaɓen 2023.
A wancan lokaci, G5 karkashin jagorancin Wike sun yi watsi da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, inda suka goyi bayan Tinubu na jam’iyyar APC.
Jaridar punch ta ruwaito cewar tsoffin gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Ayodele Fayose na Jihar Ekiti, Samuel Ortom na Benue, da Okezie Ikpeazu na Abia.
Ko da yake ba a bayyana cikakken abin da aka tattauna ba, rahotanni sun nuna cewa sun tattauna hanyoyin haɗin gwiwa da komawa jam’iyya mai mulki ta APC, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shure Shure bai hana Mutuwa.
In sha Allahu APC sai tariga rana faduwa.