Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) ta lashe gasar Kotun ECOWAS ta farko da aka shirya, inda ta samu kambin zakara tare da kyautar naira miliyan 5.
Gasar ta kunshi manyan makarantu takwas da ke da bangaren karatun aikin lauyan, kuma ɗaliban ABU sun nuna kwarewa da fahimta mai zurfi a muhawara da zaman kotu har suka fi kowa fice a zagayen ƙarshe.
Jami’ar Jos ce ta zo ta biyu a gasar, inda ta samu kyautar naira miliyan 3, a yayin gasar da aka gudanar a jihar Neja a ranar Asabar.
Shugaban Kotun ECOWAS, Ricardo Gonçalves, ya jinjinawa dukkan mahalarta gasar, yana mai cewa wannan gasa ta bayyana irin zurfin ilimi da kwazon matasan lauyoyi a yankin Afirka ta Yamma.
