Babbar kotun tarayya da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Musa Umar ta yi watsi da buƙatar Gwamnatin Tarayya na kama Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Gwamnatin na tuhumar ta da bacin suna a madadin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
Lauyan gwamnati, David Kaswe, ya nemi kotu ta bayar da sammaci bayan wadda ake tuhuma ta gaza bayyana a kotu. Amma kotun ta ƙi amincewa da buƙatar kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
