Wednesday, April 8, 2026
HomeSiyasaShiga jam'iyyar APC tamkar cin amanar mutanena ne - Gwamna Mutfwang

Shiga jam’iyyar APC tamkar cin amanar mutanena ne – Gwamna Mutfwang

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya yi watsi da rahotannin da ke cewa zai fice daga jam’iyyar adawa ta PDP, zuwa jam’iyyar APC.

Gwamnan ya ce zai ci gaba da zama a jam’iyyarsa ta PDP, yana mai cewa barin jam’iyyar zai zama kamar cin amanar jama’arsa ne.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa an yi ta samun kiraye-kiraye na wasu kungiyoyi a cikin jam’iyyar APC na neman gwamnan ya koma jam’iyyar.

Kiraye-kirayen ya farune bayan da gwamnoni biyu da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP kwanan nan suka koma APC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata