Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya daga ziyarar aiki da zai yi a jihar Kaduna,a maimakon haka, zai je jihar Binuwai a ranar Laraba 18 ga watan Yuni, 2025, a wani bangare na yunkurin samar da zaman lafiya da magance rigingimun da suka addabi al’ummar jihar.
Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
A cewarsa ziyarar shugaban Tinubu na da nufin duba yadda rikicin da ya sa mutane dadama rasa rayukansu.
