Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiNijeriya na daga cikin Kasashe 12 da Ke fuskantar barazanar Yunwa —...

Nijeriya na daga cikin Kasashe 12 da Ke fuskantar barazanar Yunwa — MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana Nijeriya da wasu kasashe 11 a matsayin wadanda ke fuskantar hadarin yunwa mai tsanani, matukar ba a dauki matakan gaggawa ba.

A wani rahoto da Hukumar Abinci da Aikin Noma (FAO) da WFP suka fitar ranar Litinin, an bayyana cewa rikice-rikice, matsalolin tattalin arziki da sauyin yanayi suna kara jefa miliyoyin mutane cikin yunwa a duniya.

Kasashen da ke cikin hadarin mafi tsanani sun hada da Gaza, Sudan, Sudan ta Kudu, Haiti da Mali.

Rahoton ya gargadi cewa cikin watanni biyar masu zuwa, halin zai kara tabarbarewa idan ba a samar da agaji da kudaden jin kai cikin gaggawa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata