Sanata Adams Oshiomhole ya kare Majalisar Tarayya ta 10, yana mai cewa ba don su yi adawa da Shugaba Bola Tinubu aka zabe su ba.
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Oshiomhole ya ce: kimarsu ce za ta zube a idon Duniya daga randa suka ja zare da Tinubu.
Ya kalubalanci masu sukar majalisar da su ambato kowace doka da aka amince da ita wadda bata amfani da ‘yan Najeriya, yana mai cewa duk wata doka da suka amince da ita an yi muhawara sosai akanta.
